1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso ta shiga kafar wando guda da Human Rights Watch

Abdoulaye Mamane Amadou
April 28, 2024

Kasar Burkina Faso ta yi watsi da zarge-zargen kungiyar kare hakin bil'adama na Human Rights Watch kan kisan fararen hula fiye da 200 a yankunan Nodin da Soro na arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/4fH9f
Shugaba Ibrahim Traore na kasar Burkina Faso
Shugaba Ibrahim Traore na kasar Burkina FasoHoto: Alexey Danichev/AFP

Gwamnatin Burkina Faso ta yi fatali da zarge-zargen da kungiyar kare hakin bani'adama ta Human Rights Watch ta yi mata na kisan fararen hula fiye da 220 a yankin arewacin kasar.

Karin bayani:Ana zargin sojojin Burkina Faso da kashe fararen hula 223

A cikin wata sanarwar da ta fitar a karshen wannan mako, gwamnatin Burkina ta bayyana zargin da wani maras tushe, tana mai cewa tuni ma ta kafa wani kwamitin bincike kan batun kisan fararen hular a yankunan Nodin da Soro na arewacin Burkina Faso.

A ranar Alhamis din da tagabata ne dai kungiyar kare hakin bani Adama ta Human Rights Watch, ta zargi dakarun gwamnatin Burkina Faso da zartar da hukuncin kisa kan fararen hula 223 da gangan ciki har da kananan yara 56.

Karin bayani: Burkina Faso ta dakatar da shirye-shiryen BBC da VOA

Fiye da mutane dubu 20 ne dai suka mutu wasu akalla miliyan biyu suka tsere daga gidajensu sakamakon hare-haren kungiyoyi masu gwagwarmaya da makamai da ke da alaka da al-Qa'ida a yankuna da dama na Burkina Faso tun a shekarar 2015.